Najeriya da Thailand sun bayyana aniyarsu ta zurfafa haɗin gwiwar tattalin arziki, tare da ƙara bunƙasa harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu domin amfanin juna.

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana hakan ne yayin da Najeriya da Thailand suka r hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan hadin gwiwar fasaha a Abuja. Ambasadar ce ta sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da mataimakin Firaministan Thailand kuma Ministan Harkokin Wajen kasar, Sihasak Phuangketkeow, ya sanya hannu a madadin Thailand.

Ministar ta yi maraba da shirin Thailand-Africa Initiative, tare da yin kira da a kara hadin gwiwa tsakanin Nigerian Technical Aid Corps da Thailand International Cooperation Agency. Ta ce hakan zai taimaka wajen bunkasa kwarewar ma’aikata, musayar fasaha da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Ta kuma yaba da aikin hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Thailand kan bunkasa fasahar noma mai dorewa, inda ta bukaci a fadada aikin zuwa wasu sassan Najeriya. Ta ce akwai bukatar kara hadin gwiwa wajen binciken noma, kirkire-kirkire da amfani da sabbin fasahohi.

Ambasada Odumegwu-Ojukwu ta ce Najeriya na son daga dangantakarta da Thailand zuwa matakin kawancen dabarun hadin gwiwa, inda tattalin arziki zai kasance daya daga cikin muhimman ginshikansa. Ta kuma bukaci a fadada cinikayya fiye da danyen mai, shinkafa da injinan noma, zuwa masana’antu, makamashi, fasahar sadarwa, hakar ma’adinai da makamashi mai sabuntawa.

Ta jaddada cewa Najeriya na da babbar kasuwar masu amfani da kayayyaki da kuma damarmakin zuba jari, tana mai kira ga kamfanonin Thailand da su yi amfani da damar da kasar ke bayarwa. Ta kuma nemi a kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu domin sa ido kan aiwatar da yarjejeniyoyi da kuma hanzarta kammala yarjejeniyoyin da suka rage, ciki har da na kare zuba jari da bunkasa cinikayya.

Najeriya ta kuma bukaci a kara hadin gwiwa tsakanin kungiyar kasashen Kudu maso Gabashin Asiya, ASEAN, da kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka domin bude sabbin damar kasuwanci, zuba jari da ci gaba. A nasa bangaren, mataimakin Firaministan Thailand, Sihasak Phuangketkeow, ya ce kafa kawancen tattalin arziki tsakanin kasashen biyu zai kara bunkasa zuba jari da cinikayya, tare da inganta rayuwar al’ummomin kasashen biyu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *