Asusun Raya Ababen More Rayuwa na Gas da Tacewa, MDGIF, ya ce ya taimaka wajen jawo jarin sama da Naira tiriliyan 1.6 cikin ayyukan iskar gas 31 a Najeriya.
Asusun ya ce jarin ya shafi kadarorin samar da ababen more rayuwa 205, da suka haɗa da ayyukan da za su taimaka wajen faɗaɗa amfani da iskar gas wajen sufuri, masana’antu da kuma gidaje.
- Tinubu ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Legas, Oba Akiolu
- Zamfara APC na fuskantar rikici yayin da ’yan majalisa bakwai suka fice daga jam’iyyar
A halin yanzu, an ce tashoshin CNG guda tara sun fara aiki a Legas, Abuja, Owerri da Ile-Ife, yayin da ake sa ran wasu ayyuka kusan 50 za su kammala ko fara aiki kafin ƙarshen shekarar 2026.
MDGIF ya ce tallafawa irin waɗannan ayyuka na daga cikin matakan da ake ɗauka wajen faɗaɗa ababen more rayuwa na iskar gas da kuma ƙara amfani da iskar gas a cikin gida.
Hakan na zuwa ne yayin da Najeriya ke ƙoƙarin amfani da dimbin albarkatun iskar gas da take da su wajen bunƙasa masana’antu da sufuri, tare da samar da hanyoyin makamashi ga ’yan ƙasa.