Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, a fadarsa ta Iga Idunganran da ke Legas Island.
A yayin ziyarar, Oba Akiolu ya yi wa Shugaba Tinubu da gwamnatinsa addu’a, tare da ba shi shawarwari kan harkokin ƙasa da jin daɗin al’ummar Najeriya.
Shugaban Ƙasar ya samu tarba daga iyalan gidan sarautar da kuma dimbin mazauna yankin da suka fito domin tarbarsa.
- ’Yan sandan FCT sun gargadi masu ababen hawa kan motocin da ba su da lamba
- Zamfara APC na fuskantar rikici yayin da ’yan majalisa bakwai suka fice daga jam’iyyar
Magoya bayan APC da sauran masu yi wa shugaban fatan alheri sun cika titunan Marina da Isale Eko yayin da ayarin motocinsa ke isa fadar.
Tinubu ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da wasu manyan ’yan jam’iyyar APC da abokan siyasa.
Ziyarar na daga cikin tarukan da Shugaba Tinubu ke yi da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki tun bayan dawowarsa Legas daga hutun aiki.
Ganawar ta kuma ƙara ƙarfafa hulɗa tsakanin gwamnatin tarayya da cibiyar sarautun gargajiya, musamman wajen tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa da jin daɗin jama’a.
