Rundunar ’Yan Sandan Abuja ta gargadi masu ababen hawa da su guji amfani da motocin da ba su da ingantacciyar lambar mota, motocin da aka yi wa gilashi duhu ba tare da izini ba, da kuma motocin da aka ɓoye ko lalata lambobinsu.

Kwamishinan ’Yan Sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya bayar da umarnin kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana karya dokokin, yana mai cewa irin waɗannan motoci na iya sauƙaƙa wa masu aikata laifuka ɓoye kansu daga jami’an tsaro.

Rundunar ta kuma yi gargaɗi kan amfani da lambobin diflomasiyya na bogi ko kuma amfani da irin waɗannan lambobi ba tare da izini ba.

Kwamishinan ya umarci jami’an ’yan sanda a faɗin Abuja da su tsaurara bincike da tabbatar da bin dokokin da suka shafi lambobin motoci da amfani da gilashin duhu, tare da gargadin jami’ai kada su yi amfani da aikin wajen karɓar kuɗin haram.

Rundunar ta kuma buƙaci mazauna Abuja su taimaka wajen tabbatar da tsaro ta hanyar kai rahoton motocin da ake zargi ko wasu abubuwan da ba su dace ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *