Kamfanin Dangote Group ya ce ƙara samar da kayayyaki a cikin gida na da muhimmanci wajen ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya da rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje.
Manajan Kamfanin, Abdullahi Bello Danmusa, ya bayyana hakan ne a wajen rana ta musamman ta Dangote a Abuja International Trade Fair, inda ya ce cinikayya na da amfani sosai idan ƙasar na da ƙarfi wajen samar da kayayyaki a cikin gida.
Ya ce Najeriya na buƙatar ƙara saka jari a masana’antu domin samar da ayyukan yi, tallafa wa ’yan kasuwa da kuma rage matsin lambar da dogaro da shigo da kayayyaki ke haifarwa.
- ’Yan sandan FCT sun gargadi masu ababen hawa kan motocin da ba su da lamba
- Ambaliyar ruwa ta shafi gidaje 143 a Damaturu
Danmusa ya ce Dangote Group na ci gaba da saka jari a fannoni daban-daban da suka haɗa da siminti, sukari, taki, kayan marufi, sinadarai da tace man fetur.
Ya ce makomar juriyar tattalin arzikin Najeriya za ta dogara ne kan yadda ƙasar za ta ƙarfafa iya samarwa, yin gasa da kuma fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Abuja wato Chamber of Commerce and Industry, ACCI, Farfesa Adebisi Adesugba, ya yaba wa Dangote kan gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa masana’antu, samar da ayyukan yi da rage dogaro da shigo da kayayyaki.
Ya ce haɗin gwiwar ACCI da Dangote na taimakawa wajen samar da damarmaki ga ’yan kasuwa da masu zuba jari, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.