Hoto: NAN

Magajin birnin New York, Zohran Mamdani, ya yaba da irin tasirin al’adun Najeriya a duniya, yana mai cewa birnin New York ma yana amfana da gudunmawar ’yan Najeriya da ke zaune a cikinsa.

Mamdani ya bayyana haka ne a wajen bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai da aka gudanar a New York, inda ya ambaci tasirin wakokin Najeriya, da abinci da kuma ƙwallon ƙafa.

Ya ce tun yana yaro yana sauraron wakokin ’yan Najeriya, inda ya ambaci Runtown da Patoranking a matsayin wasu daga cikin mawakan da ya sani.

Magajin New York ya kuma ce ’yan Najeriya da ke zaune a birnin sun taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma, yana mai cewa gudunmawarsu ta taimaka wajen sanya New York ta zama abin alfahari.

A nasa jawabin, Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce bikin ya zama wata dama ta sake jaddada muhimmancin haɗin kai, zaman lafiya da gina ƙasa.

Ya kuma bayyana ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje a matsayin wani muhimmin ginshiƙi na ƙarfin Najeriya a duniya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *