Masu zaɓen sarki a Gundumar Langai dake Ƙaramar Hukumar Mangu a jihar Filato sun buƙaci Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Masarautu da ya gaggauta ba da takardar naɗin sarauta dake tabbatar da zaɓen sabon Hakimin Gundumar Langai.

An gudanar da zaɓen ne a ranar Talata 19/5/2026 a ofishin Majalisar Gargajiya da ke Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Mangu.

Masu zaɓen sarkin sun bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da suka aike wa kwamishinan, wadda ta samu sanya hannun Mallam Abdullahi Haruna (Madakin Langai); da Alhaji Tijjani Yusuf Sambo (Galadiman Langai); da Idris Danbaba (Pakachin Langai); da Mr. John Tamba Tagwai (Tikam Langai) da kuma Sunusi Ibrahim Sambo (Barayan Langai).

Masu zaɓen sarkin sun jaddada cewa rashin samun shugaban gunduma da aka amince da shi a hukumance ya haifar da giɓin shugabanci dake shafar gudanar da harkokin al’umma yadda ya kamata.

“Wannan giɓin idan aka yi la’akari da halin da ake ciki, ya fi shafar fannin tsaro da kuma buƙatar samun shugabancin gargajiya don sasanta rikice-rikice, da yin mu’amala da hukumomin tsaro, da kuma tafiyar da ayyukan gwamnati a matakin gundumomi,” in ji wasiƙar.

“Rashin Hakim na dindindin a gunduma na taka muhimmiyar rawa wajen samun damar magance waɗannan matsaloli cikin sauri da inganci.”

“Naɗi da kuma amincewa da Hakimin gunduma a hukumance zai samar da ingantaccen tsarin shugabanci, da kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin al’umma da ƙaramar hukuma, da hukumomin tsaro, da gwamnatin jiha, tare da dawo da ƙwarin gwiwar jama’a kan gudanar da sarautar gargajiya.

“Don haka, muna roƙon ofishin ka cikin mutuntawa da ya gaggauta ɗaukar matakin bayar da takardar naɗin Hakimin Gundumar Langai da aka zaɓa bisa ƙa’ida, tunda an cika dukkan sharuɗɗan da suka dace.

Masu zaɓen sarkin sun ƙara da cewa “Muna yin wannan roƙo ne don samar da zaman lafiya, da tsaro, da kwanciyar hankali, da ci gaba da bunƙasa gundumar Langai da Ƙaramar Hukumar Mangu. Muna da ƙwarin gwiwa kan ƙudurin gwamnatin Jihar Filato na karewa da ƙarfafa masarautun gargajiya a faɗin jihar.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *