Najeriya da Masarautar Jordan ta Hashemite sun sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro, musayar bayanan sirri da kuma yaƙi da ta’addanci.
Ƙaramin Ministan Tsaro na Najeriya, Bello Matawalle ne ya Sanya hannu a madadin Najeriya
- Majalisar Dattawa ta nesan ta kanta da umarnin kama Mele Kyari
- Kungiyoyin Fararen Hula sun yi zanga-zanga kan rashin tsaro
- Abuja na cigaba da samun Sabbin Tituna-Mariya Bunkure
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Amman, inda ta ƙunshi horas da sojoji tare, bincike da ci gaban fasahar tsaro, haɗin gwiwa a ma’aikatun tsaro da kuma tabbatar da tsaron yankuna.
Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban ci gaba a dangantakar ƙasashen biyu, yana mai jaddada cewa musayar fasaha da bunƙasa ƙwarewar tsaro na daga cikin manyan abubuwan da aka fi baiwa fifiko