Masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa yaduwar ƙwayoyin cuta masu jure maganin rigakafi na ƙara zama babbar barazana ga lafiyar al’umma a duniya.
Jurewar ƙwayoyin cuta ga maganin rigakafi na faruwa ne lokacin da ƙwayoyin cuta suka samu damar tsira daga magungunan da ake amfani da su wajen kashe su.
Hakan na sa cututtuka su zama masu wahalar magani, tare da buƙatar amfani da magunguna masu ƙarfi da tsada.
A cewar bayanan masana kiwon lafiya, yawan amfani da magungunan rigakafi ba tare da buƙata ba, da kuma amfani da su ba daidai ba a wajen kula da mutane da noma da kiwon dabbobi, na daga cikin abubuwan da ke ƙara haifar da wannan matsala.
- Matsalar tabin hankali tsakanin matasa na ƙara zama abin damuwa a duniya
- Tamowa a Sokoto: Yara na fuskantar barazanar rashin abinci mai gina jiki
Misali, wasu mutane kan shan maganin rigakafi wajen magance cututtukan ƙwayoyin cuta kamar mura, alhali irin waɗannan magunguna ba sa magance cututtukan da ƙwayoyin cuta ke haddasawa.
Haka kuma, rashin kammala shan maganin da aka rubuta na iya taimaka wa ƙwayoyin cuta su saba da maganin.
Wasu ƙwayoyin cuta masu haɗari, na ƙara zama matsala a asibitoci a sassan duniya.
Ƙasashe masu tasowa na fuskantar ƙarin haɗari saboda ƙarancin samun ingantaccen kiwon lafiya da tsaftar muhalli, yayin da jabun magunguna ko waɗanda ba su da inganci ke ƙara dagula lamarin.
Masana kiwon lafiya na kira da a tsaurara dokokin amfani da magungunan rigakafi, a inganta tsaftar muhalli, sannan a ƙara zuba jari wajen bincike da samar da sabbin magunguna.
Haka kuma, ana buƙatar jama’a su guji shan maganin rigakafi da kansu, su yi amfani da shi ne kawai bisa shawarar ƙwararren ma’aikacin lafiya, sannan su kammala tsarin maganin da aka ba su.
Idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, duniya na iya fuskantar wani yanayi da ake kira “post-antibiotic era”, inda ko ƙananan cututtuka za su iya zama masu haɗarin kisa saboda magungunan da ake da su ba sa iya yakar ƙwayoyin cutar.