Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP, Mista Olatunji Disu

Sufeta Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP, Mista Olatunji Disu, ya bayyana cewa shirye-shiryen ɗaukar sabbin ‘Yan Sanda 50,000 ya kai matakin ƙarshe na kafin horarwa.

A cewar sa, an kammala tsara cikakkun shirye-shiryen horarwa bisa sabon tsarin karatu da kuma bin ƙa’idoji na ƙasa da ƙasa.

IGP Disu ya sake jaddada ƙudurin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da kare al’umma da kare hakkin bil’adama da kuma kiyaye bin doka.

Sufetan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, a Washington, D.C. dake Amurka, yayin da yake wakiltar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a taron karo na 2 na kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya kan ƙasashen da ke da damuwa ta musamman.

Disu ya jaddada muhimmancin haɗa kai da al’umma wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, inda ya ce ‘yan sanda sun ci gaba wajen haɗin kai da sarakunan gargajiya, shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, amincewar jama’a tsayuwar addini wajen wanzar da zaman lafiya suna da matuƙar muhimmanci wajen samun tsaro mai ɗorewa a faɗin Najeriya.

Disu na daga cikin manyan tawagar Najeriya da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, NSA, ya jagoranta. Tawagar ta hada da Ministocin Harkokin Waje, Cikin Gida da Tsaro, shuwagabannin Sojoji, da shugabannin sauran hukumomin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *