Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata satar babur mai ƙafa uku, tare da kwato babur ɗin da kuma bindigogi ƙirar gida guda biyu.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne bayan wasu mutane sun yi hayar babur ɗin daga unguwar Hotoro da ke Kano zuwa Yar Gaya a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, kan kuɗin haya na N8,000.

Rundunar ta ce yayin da suke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, waɗanda ake zargin sun fito da bindigogi suka yi wa direban barazana tare da kwace babur ɗin.

Bayan samun rahoton, rundunar ta ce ta fara gudanar da bincike da ayyukan leƙen asiri bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.

Daga bisani, jami’an ’yan sanda na sashen Filin Hockey suka gano babur ɗin a ranar 3 ga Oktoba a Wudil, a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri.

Rundunar ta ce an kama Abubakar Isah, mai shekaru 27, da Shehu Ibrahim, mai shekaru 25, waɗanda dukkansu mazauna ƙauyen Zogarawa ne a Dawakin Kudu.

An kuma kwato babur ɗin da ake zargin an sace da bindigogi ƙirar gida guda biyu. ’Yan sandan sun ce waɗanda ake zargin sun amsa hannu a aikata laifin yayin bincike.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da kira ga mutanen da suka taɓa fuskantar irin wannan fashi a yankin Hotoro zuwa Dawakin Kudu da Wudil da su tuntubi sashen ’yan sanda na Filin Hockey domin taimakawa wajen gano sauran waɗanda ake zargi.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *