Yayin da ake gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti, an samu rahotanni da dama daga masu zaɓe a faɗin jihar kan zargin sayen ƙuri’u.
Wani rahoto ya nuna cewa ana ba wa masu zaɓe kuɗi har Naira 5,000 domin su zaɓi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC). Wannan zargi ya jawo damuwa kan gaskiya da adalcin zaɓe, domin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tana ɗaukar sayen ƙuri’u a matsayin laifin zaɓe.
A wani bidiyo da masu sa ido na Dataphyte suka wallafa daga ƙaramar hukumar Ado, musamman a D’Ugbo Ward 4, Rumfar Zaɓe ta 2 (Makarantar Firamare ta St. Michael, kusa da gidan mai na Mobil), an ga wani wakilin jam’iyya yana rubuta bayanan masu zaɓe kamar lambobin asusun banki da lambobin waya tare da neman shaidar cewa sun kaɗa ƙuri’a. A cewar masu sa ido, ana zargin wakilin yana ba da Naira 10,000 ga kowane mai zaɓe.
A ƙaramar hukumar Ilejemeje ma, wani mai sa ido ya sanar da Dataphyte cewa an samu wani zargin sayen ƙuri’u. A cewarsa, an ga wani wakilin jam’iyyar APC yana tattaunawa da masu zaɓe bayan sun gama kaɗa ƙuri’arsu. Bayan haka, yana ba su ƙananan takardu masu lambobi. Sai dai Dataphyte ta ce ba ta samu damar tabbatar da dalilin wannan hulɗa ko amfanin takardun ba.
An kuma samu irin wannan rahoto a yankin kasuwar Eleyowo/Odoba Gidado, inda masu sa ido suka ce sun ga wakilan APC suna kai masu zaɓe zuwa wani keɓaɓɓen wuri domin ba su kuɗi. Haka kuma, a wuraren zaɓe daban-daban da suka haɗa da Odo Emure 1, Iye da yankin shagon Peter Adesina, an ruwaito cewa wakilan APC na ba masu zaɓe kuɗi ko wasu kyaututtuka domin su zaɓi jam’iyyar.
- Zaben EKiti: Dan Takarar Gwamna na jam’iyyar PDP Dakta Wole ya zargi ana tsoratar da masu kada kuri’a
- EKiti 2026: Meyasa Ekiti ke gudanar da zaben ta da ban da sauran Jihohi
- Zaɓen Gwamnan Ekiti: Tarihin siyasa da yanayin hamayya a jihar
A rumfar zaɓe ta Ilegbio da ke ƙaramar hukumar Oye, an kuma ga wani wakilin APC yana magana da masu zaɓe bayan sun kaɗa ƙuri’arsu tare da ba su takardu masu lambobi. Sai dai ba a samu tabbacin dalilin bayar da waɗannan takardu ba.
A rumfar zaɓe da ke Makarantar Firamare ta St. Michael a harabar Olubobokun, an kuma ga wani wakilin APC yana tattara sunaye, lambobin waya da bayanan asusun wasu masu zaɓe. An kuma ce an buƙaci waɗannan mutane su nuna shaidar cewa sun yi zaɓe. Rahotanni daga wurin sun nuna cewa ana yi musu alƙawarin Naira 10,000, amma Dataphyte ba ta tabbatar da wannan zargi ba a lokacin da aka bayar da rahoton.
Wani mai sa ido a Makarantar Firamare ta St. Silas II, Egboigidi, a gundumar Omu Oke 1 da ke ƙaramar hukumar Ekiti Ta Yammaa, ya kuma bayar da rahoton zargin sayen ƙuri’u da APC ke yi. A cewarsa, bayan mutane sun yi zaɓe, ana kai su bayan rumfar zaɓe inda ake ba su wasu lambobi na musamman. Ya kuma yi zargin cewa wasu jami’an ’yan sanda suna nuna goyon baya ga wannan aiki, yana mai cewa:
“Da alama ’yan sanda suna tare da su. Kamar dai suna jiran nasu kason ne.”
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC, Dare Bejide, shi ma ya nuna rashin jin daɗinsa bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓa ta 2, Unit 4, Ilawe Ekiti da ke ƙaramar hukumar Ekiti Ta Yamma. A wata hira kai tsaye da gidan talabijin na Channels TV, ya yi zargin cewa an samu maguɗi iri-iri ciki har da sayen ƙuri’u da kuma tsoratar da masu zaɓe.
Ya ce wakilan jam’iyyu sun zo da tarin kuɗi domin rinjayar masu zaɓe. Haka kuma ya zargi wani Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman da cin zarafinsa yayin zaɓen.
A cewarsa:
“Na zo nan ne domin in yi zaɓe kamar yadda doka ta tanada. Wannan ita ce rumfar zaɓena. A yayin da nake nan, wani mai riƙe da muƙamin siyasa mai suna Makinde ya zo tare da wani ɗan sanda na bogi. Sun ture ni, sun doki direbana sosai, sannan suka ci zarafin jami’an tsarona. Sun kuma kawo kuɗi masu yawa domin rabawa mutane. Na gaya musu cewa hakan bai dace ba domin yau ranar zaɓe ce, kuma wannan na iya haddasa wannan rikici. Wannan ba rumfar zaɓensa ba ce, amma ya ƙi tafiya.”
A ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta Najeriya, sayen ƙuri’u da kuma yin kamfen a ranar zaɓe duka laifuffuka ne. Duk wanda aka samu da laifi zai iya fuskantar tara ko hukuncin ɗaurin kurkuku.
An kuma samu wasu rahotanni na zargin rinjayar masu zaɓe da katsalandan a wuraren zaɓe daban-daban a ƙananan hukumomin Ekiti East, Ido/Osi, Ijero, Ikere da Ado.
Mafi yawan zarge-zargen sun shafi wakilan jam’iyyu da ke tattara bayanan sirri na masu zaɓe, ba su lambobi ko wasu alamomi na musamman, tare da zargin bibiyar su bayan sun kaɗa ƙuri’arsu.
