Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin tarayya na faɗaɗa cibiyoyin haɗin gwiwa na ƙananan sana’o’i (MSME hubs), domin bai wa ’yan kasuwa damar amfani da na’urori, da wutar lantarki da wuraren samar da kayayyaki ba tare da ɗaukar dukkan nauyin kuɗin kafa masana’anta da kansu ba.

Tinubu ya ce tela bai kamata ya kashe miliyoyin naira kafin ya samu injinan da za su taimaka masa faɗaɗa sana’arsa ba, haka kuma mai sarrafa abinci bai kamata sai ya gina katafaren masana’anta kafin ya iya samar da kayayyaki da yawa ba.

A cewar shugaban, gwamnati ta riga ta kafa cibiyoyin haɗin gwiwa 21 a jihohi 19 da Abuja, waɗanda ke bai wa ƙananan ’yan kasuwa damar samun kayan aiki da sauran abubuwan da za su taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu.

Tinubu ya ce cibiyoyin na daga cikin tsarin gwamnatin sa na tallafa wa ƙananan sana’o’i, da rage kuɗin gudanar da kasuwanci da kuma samar da damar ƙirƙirar ayyukan yi.

Ya ƙara da cewa ’yan Najeriya na da basira, da ƙwarewa da jajircewar gina sana’o’in da za su yi nasara, abin da gwamnati ke buƙata shi ne ta rage musu matsalolin da ke hana su bunƙasa.

A baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta kuma sanar da gina Cibiyar Bunƙasa Sana’o’i ta Abuja da tallafin dala miliyan 12 daga Koriya ta Kudu, domin samar da wuraren aiki, da fasaha, da horo da sauran tallafin kasuwanci ga ’yan kasuwa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

One thought on “Za a faɗaɗa cibiyoyin MSME domin rage wa ƙananan ’yan kasuwa kuɗin fara sana’a – Tinubu”
  1. Do you mind if I quote a few of your posts as long as I provide credit and sources back to your webpage?
    My website is in the exact same niche as yours and
    my visitors would definitely benefit from a lot of the information you present here.
    Please let me know if this alright with you. Thank you!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *