Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a fadarsa da ke Sakkwato, tare da abokin takararsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da sauran mambobin tawagarsa.
Obi ya ce sun yi amfani da ziyarar wajen jajanta wa Sarkin Musulmi bisa rasuwar Sardaunan Sakkwato, tare da tattauna wasu muhimman batutuwan da suka shafi makomar Najeriya.
A cewar Obi, ya jaddada buƙatar haɗa kan ’yan Najeriya, da inganta tsaro, da yaƙi da talauci, da samar da ayyukan yi da kuma dawo da amincewar jama’a ga ƙasar.
- Najeriya a shekaru 66: Shin tsarin kiwon lafiya ya inganta yadda ya kamata?
- ’Yan takarar ADC daga jihohi huɗu sun koma APC
- Zaben 2027: Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya umarci jami’ai su kasance a tsaka-tsaki
Ya ce Sarkin Musulmi ya tunatar da su cewa jagoranci nauyi ne daga Allah, kuma shugabanni za su kasance masu alhakin abin da suka aikata.
Obi ya kuma ce Sarkin ya bayyana tsaro, da talauci da samar da ayyukan yi a matsayin muhimman abubuwan da ya kamata a ba su fifiko.
Ya ce Sarkin Musulmi ya kuma jaddada cewa bambancin kabilu, da harsuna da addinai da ke Najeriya ya kamata ya zama ƙarfin ƙasar, ba abin raba kan jama’a ba.
Ya ce manufarsu ita ce gina Najeriya inda kowane ɗan ƙasa zai samu tsaro, da damar bunƙasa da jin cewa yana da matsayi a ƙasar.
Ziyarar ta zo ne a lokacin da ’yan siyasa ke ƙara gudanar da shawarwari da ganawa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki gabanin zaɓen 2027.