Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce za ta magance matsalolin aiki da dabaru tun kafin babban zaɓen 2027, domin kauce wa duk wani kuskure da zai iya rage amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya bayyana hakan a Kaduna yayin taron tantance shirye-shiryen zaɓen 2027 na shiyyar Arewa maso Yamma.
Ya ce nasarar zaɓe ba ta dogara da abin da ake yi a Abuja kaɗai ba, domin mafi muhimmanci shi ne yadda jami’an zaɓe za su gudanar da ayyukansu a ƙananan hukumomi, da rumfunan zaɓe da wuraren rajista.
- Zaben 2027: Kwamishinan ’Yan Sandan Kano ya umarci jami’ai su kasance a tsaka-tsaki
- Najeriya a shekaru 66: Shin tsarin kiwon lafiya ya inganta yadda ya kamata?
Hukumar ta ce sama da mutum miliyan 10.7 ne suka yi sabuwar rajista a matakai uku na ci gaba da rajistar masu zaɓe, yayin da aka tsara fara karɓar sabbin katunan zaɓe, PVC, daga ranar 9 ga Oktoba 2026.
Amupitan ya kuma gargaɗi jami’an zaɓe da su guji nuna bangaranci ko sakaci, yana mai cewa rashin nuna adalci, da jinkirin buɗe rumfa ko matsalar fasaha da ba a magance ba na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
Yayin da INEC ke ci gaba da shirye-shiryen 2027, babban abin da ake jira shi ne yadda za a mayar da waɗannan matakai daga takardu da taruka zuwa aikace-aikacen da ɗan ƙasa zai gani a rumfar zaɓe tun daga karɓar PVC cikin sauƙi zuwa gudanar da zaɓe cikin tsaka-tsaki da bin ƙa’ida.