Jam’iyyar ADC ta musanta ikirarin APC na cewa wasu daga cikin ’yan takararta na Majalisar Dokokin Jihohi daga Jigawa, da Plateau, da Taraba da Zamfara sun sauya sheƙa zuwa APC.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran ADC na Ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce mutanen da APC ta gabatar ba ’yan takarar ADC ba ne, kuma ba shugabannin jam’iyyar ba ne.
- Peter Obi ya ziyarci Sarkin Musulmi a Sakkwato
- INEC ta fara gyara kura-kuran da za su iya kawo cikas ga zaɓen 2027
ADC ta ƙalubalanci APC da ta bayyana mukamai ko ƙananan hukumomi da waɗannan mutane suka wakilta a matsayin ’yan takarar jam’iyyar, tare da bayar da hujjar sahihancin takardun da aka ce suna da su.
Wannan martani ya biyo bayan rahotannin cewa wasu ’yan takarar ADC daga jihohin huɗu sun bayyana komawarsu APC tare da ayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Rigimar ta ƙara nuna yadda sauya sheƙa da sabanin bayanai tsakanin manyan jam’iyyun siyasar Najeriya ke ƙara ɗaukar hankali yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.