A wani taro na ba-zata da ya girgiza birnin Minnesota na ƙasar Amurka, miliyoyin mutane ne suka taru a ƙarƙashin inuwar tafiyar “No Kings” domin nuna rashin amincewarsu da yadda suke ganin darajar Amurka tana raguwa a idon duniya.
Taron, wanda ya samu halartar fitaccen Sanata mai rajin kare haƙƙin talakawa, Bernie Sanders, ya janyo hankulan masana siyasa da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, inda aka tattauna matsalolin da suke taba ginshiƙan demokradiyyar ƙasar.
Manufar tafiyar ‘No Kings’ ita ce yaƙi da mulkin danniya na ɓangaren masu ra’ayin riƙau a karkashin shugabancin Donald Trump.
A cewar Sanata Sanders, hakan na nuni ne ga babban tsoron da Amurka ke da shi na komawa tsarin mulkin mallaka ko na kama-karya.
Waɗanda suka shirya gangamin suna iƙirarin cewa masu fada-a-ji, da manyan kamfanoni da attajirai sun mamaye siyasar ƙasar, lamarin da ya sa muryar talaka ba ta da tasiri.
Kana akwai gibi mai girma tsakanin masu kuɗi da talakawa, wanda babbar barazana ce ga zaman lafiyar Amurka a cikin gida.
A ɓangaren manufofi da suka shafi ƙetare, sun nuna cewa maimakon Amurka ta kasance jagora wajen samar da zaman lafiya, ta koma tana ƙara tsunduma cikin yaƙe-yaƙe marasa tasiri ga ƙasar.
A jawaban da ya gabatar, Sanata Bernie Sanders ya jaddada bukatar yin garambawul ga tsarin tattalin arzikin Amurka.
“Ba za mu iya ci gaba da kiran kanmu jagorar duniya ba alhali miliyoyin ‘yan ƙasarmu ba su da inshorar lafiya, kuma ba su da ikon biyan bukatunsu na yau da kullum.
“Kuma Amurka ba ta kan tsarin mulukiyya, ta talakawa ce zalla.”
Sanders ya yi nuni da cewa raguwar darajar Amurka a duniya ba wai saboda rashin ƙarfin soja ba ne, gazawarta ne wajen samar da adalci ga kowa a cikin gida.
Masharhanta na ganin wannan taro ya nuna alamun cewa Amurka na fuskantar wani babban sauyi na tunani, da suka haɗar da rage tallafi ga kasashen waje, da sauya tunanin masu jefa kuri’u.