Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bukaci Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) da ya tabbatar da cewa kudaden da gwamnati ta ware wa ɗalibai sun isa hannun waɗanda aka tanada musu, tare da ƙarfafa matakan hana karkatar da kudaden.
Olukoyede ya bayyana hakan a Abuja yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin EFCC da NELFUND.
- Rundunar sojin Najeriya ta sake jaddada ƙudirin kare muhimman ababen more rayuwa na makamashi
- EFCC ta nemi limmai da fastoci su ƙara ƙyaimi wajen yaƙi da cin hanci
Ya ce ya kamata a fi mayar da hankali kan hana almundahana tun kafin ta faru, maimakon jira sai an sace kuɗi sannan a fara bincike.
Olukoyede kuma bukaci NELFUND ta ƙara amfani da tsarin biyan kuɗi kai tsaye ga ɗaliban da aka tantance, domin rage shiga tsakani da damar yin magudi.
A nasa bangaren, shugaban NELFUND, Akintunde Sawyer, ya ce asusun ya karɓi aikace-aikacen lamuni miliyan 1.6, inda aka amince da 960,000.
Ya ce ana biyan ɗalibai kai tsaye ta asusun bankinsu bayan tantance bayanansu.