Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Muhammad Idris, ya ce Najeriya na maraba da ƙarin masu zuba jari da ’yan kasuwa daga Saudiyya, yayin da ƙasashen biyu ke ƙara zurfafa dangantakar da ke tsakaninsu.
Muhammad Idris ya bayyana hakan ne a wajen liyafar bikin cika shekaru 96 da Ranar Ƙasa ta Masarautar Saudiyya, wadda Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousuf bin Mohammed AlBalawi, ya shirya.
- EFCC ta gargadi NELFUND kan kudaden tallafin ɗalibai
- Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Troost-Ekong, ya karɓi Musulunci a Qatar
Ministan ya ce Najeriya da Saudiyya na da damar ƙara haɗin gwiwa fiye da dangantakar da aka saba da ita, musamman a fannonin noma da samar da abinci, da makamashi, ababen more rayuwa, ma’adinai da fasaha.
Taron ya samu halartar Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo.
Muhammad Idris ya taya gwamnatin da al’ummar Saudiyya murnar cika shekaru 96 da Ranar Ƙasar, tare da jaddada buƙatar ƙara bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Najeriya da Saudiyya.