Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar wa mazauna babban birnin tarayya cewa za a kammala aikin hanyar Apo-Karshi da Bwari-Kubwa kafin ƙarshen Disamba 2026, domin buɗe su ga jama’a.
Wike ya bayyana hakan ne bayan duba ayyukan raya ababen more rayuwa a wasu garuruwan da ke wajen tsakiyar Abuja.
Ya ce aikin hanyar Apo zuwa Karshi, wanda aka fara ba da kwangilarsa tun 2010, ya daɗe yana fuskantar tsaiko kafin a soke tsohuwar kwangilar tare da sake ba da ita.
- Kano ta amince da mayar da PHC biyar zuwa manyan asibitoci
- Trump da Xi sun gana a Fadar White House, sun tattauna tsaro da fasahar AI
Ministan ya ce dan kwangilar ya yi alkawarin miƙa hanyar Apo zuwa Karshi a watan Nuwamba, yayin da ake sa ran kammalawa da miƙa hanyar Bwari zuwa Kubwa kafin ƙarshen shekara.
Wike ya kuma danganta ayyukan da ci gaban garuruwan da ke wajen tsakiyar Abuja, yana mai cewa gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen kai ayyukan more rayuwa zuwa waɗannan yankuna.
Dangane da zaɓen 2027, Wike ya bayyana kwarin gwiwarsa kan nasarar Bola Ahmed Tinubu da wasu ’yan takarar APC a Abuja, yana mai danganta hakan da ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa a babban birnin tarayya.
Ya kuma ce ayyukan raya ababen more rayuwa a FCT za su ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na ayyukan gwamnati kafin zaɓen 2027.