Gwamnatin Tarayya ta ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun kafa tubalin samun ci gaba da bunƙasar tattalin arziki tare da samar da wadata ga ‘yan Najeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron manema labarai na musamman da aka shirya domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
Ministan ya ce gwamnati ta gaji dimbin matsalolin tattalin arziki da na kasafin kuɗi, amma ta ɗauki matakan gyara wasu daga cikin matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, duk da cewa sauye-sauyen sun jawo wa ‘yan Najeriya wasu ƙalubale.
- Atiku ya naɗa Akobundu shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, El-Rufai ya zama mataimakinsa
- Najeriya da DP World za su zuba sama da dala biliyan 7 a tashar ruwa da ke Ogun
Ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu bunƙasar kashi 4.43 cikin ɗari a zango na biyu na shekarar 2026, daga kashi 4.23 cikin ɗari a makamancin lokacin na shekarar 2025.
Ya kuma ce an samu ci gaba wajen ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje, tace man fetur a cikin gida da kuma harkokin zuba jari.
Mohammed Idris ya kuma bayyana cewa Najeriya ta fita daga jerin ƙasashen da ke karkashin sa ido na FATF kan matsalar kuɗaɗen haram, sannan ta koma cikin JP Morgan Emerging Markets Bond Index bayan shafe shekaru 11 ba ta cikinsa ba.
Sai dai ministan ya amince cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale, musamman a fannin tsaro da kuma rage radadin rayuwa ga ‘yan ƙasa, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da cewa amfanin sauye-sauyen tattalin arzikin ya fara isa ga talakawa da sauran ‘yan Najeriya.
Shi ma Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce babban aikin da ke gaban gwamnati shi ne tabbatar da cewa ribar sauye-sauyen tattalin arziki ta koma cikin ingantattun damammaki ga talakawa.
Akume ya ce gwamnati na ƙara ƙoƙari wajen tara kuɗaɗen shiga, inganta harkokin kuɗin gwamnati da kuma zuba jari a ababen more rayuwa da noma da ilimi da lafiya da tallafin zamantakewa.
A nasa bangaren, Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce sauye-sauyen na da nufin samar da tattalin arzikin da ya fi girma kuma ya shafi jama’a da dama, yayin da Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce inganta tsaro a wasu yankunan noma ya taimaka wajen ƙara samar da amfanin gona.
Gwamnatin ta ce bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai wata dama ce ta duba nasarorin da aka samu, da ƙalubalen da ake fuskanta da kuma matakan da ya kamata a ɗauka domin gina ƙasa mai ƙarfi da tsaro da wadata ga al’umma.