Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta ce ɗaukar kaya fiye da ƙa’ida a ababen hawa ba karya dokar hanya kawai ba ce, illa matsala ce da ke barazana ga rayukan jama’a, da lafiyar ababen hawa da kuma dorewar hanyoyin Najeriya.
Wannan na daga cikin abubuwan da suka fito yayin wani taron tattaunawa na ƙasa kan illolin ɗaukar kaya fiye da kima da haɗa fasinjoji da kaya ba bisa ƙa’ida ba, wanda hukumar FRSC ta shirya a Abuja tare da ƙaddamar da shirin inganta ɗaukar kaya cikin aminci da hanyoyi masu tsaro na ƙasa.
A cewar hukumar FRSC, kaya masu yawa fiye da ƙa’ida na iya rage ingancin birki, da karkatar da sitiyari da daidaiton abin hawa, tare da ƙara lalacewar taya da sauran sassan mota da kuma haɗarin yin hatsari.
- INEC ta ce za ta fara shirye-shiryen zaɓen 2027 tun da wuri
- Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ta fara neman direban da ya haddasa tashin gobara a Kubwa
Hukumar ta ce matsalar ta kuma shafi lalacewar hanyoyi sakamakon nauyin da ya wuce ƙa’idar da aka tsara musu.
FRSC ta jaddada cewa nauyin alhakin ba ya kan direba kaɗai, domin masu kaya, masu ɗaukar kaya, kamfanonin sufuri, ma’aikatan loda kaya da hukumomin sa ido duk suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da bin ƙa’ida.
Taron ya kuma buƙaci a mayar da batun daga yin hukunci kawai kan masu karya doka zuwa wayar da kan jama’a, inganta tsarin auna nauyin kaya, da ƙarfafa sa ido da kuma haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki.
FRSC ta ce manufar ita ce a koma daga ɗaukar mataki bayan hatsari zuwa hana hatsarin faruwa tun farko.
Hukumar ta ce sakamakon wannan tattaunawa zai taimaka wajen ƙarfafa shirin wayar da kan jama’a a lokacin Ember Months, inda za a fi mayar da hankali kan ɗaukar kaya cikin aminci tare da sauran laifukan hanya kamar wuce ƙa’idar gudu da amfani da waya yayin tuƙi.
FRSC ta ce auna nasarar shirin ba zai kasance yawan tarukan da aka gudanar ba, illa yadda zai taimaka wajen rage motocin da ke ɗaukar kaya fiye da ƙa’ida, rage haɗurra, kare hanyoyi da kuma ceto rayukan masu amfani da tituna.