Muƙaddashin Babban Sakatare na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, Dr Emmanuel Ikpeme, ya buƙaci tawagar Super Eagles ta guji duk wani abin da zai ɗauke mata hankali yayin da za ta fuskanci Guinea Bissau a wasan neman gurbin shiga AFCON na 2027,a ranar Talata.
Ikpeme ya bayyana hakanne yayin da tawagar Najeriya ta sauka a Bissau da yammacin ranar Lahadi.
A jimlace, Najeriya da Guinea Bissau sun buga wasanni huɗu a hukumance a ajin manya, inda Super Eagles ta lashe uku daga cikin wasannin, yayin da Guinea Bisau ta samu nasarar lashe wasa ɗaya.
-
Najeriya ta doke Madagascar a wasan farko na neman gurbin Gasar AFCON ta 2027
-
Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Troost-Ekong, ya karɓi Musulunci a Qatar
-
NPFL: Barau FC ta ci gaba da samun nasara, yayin da Enyimba ta sha kashi a gida
A gefe guda, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka ta nada alƙalin wasa daga ƙasar Habasha don yin alƙalanci a wasan na ranar Talata, wanda zai fara daga karfe 4 na yamma agogon Guinea Bissau (karfe 5 na yamma a Najeriya).
Super Eagles, wadda ta lashe Gasar AFCON har sau uku, ta na fatan ci gaba da samun nasara a fafatawar bayan doke Madagasacar a wasan farko da ci 2-1 a wasan da suka buga a filin wasa na Godswill Akpabio a ranar Jumma’a.
George Ilenikhena da kuma Moses Usor, ne suka zura ƙwallayen da suka tabbatarwa Najeriya nasara akan Madagascar.
