Najeriya na ɗaukar babban kaso na kuɗaɗe da kayan aiki wajen gudanar da rundunar MNJTF, a yayin da ake fama da gibin kuɗi da kayan aikin yaƙi da Boko Haram da ISWAP a yankin tafkin Chadi. Wannan na zuwa ne bayan shafe kusan shekaru 17 ana fama da matsalar tayar da ƙayar baya a arewa maso gabashin Najeriya.
MNJTF runduna ce ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi Najeriya, da Kamaru, da Chadi, da Nijar da Benin, wadda aka kafa domin tunkarar Boko Haram, daga bisani kuma ta mayar da hankali kan ISWAP bayan ƙungiyar ta zama babbar barazana a yankin.
Duk da ayyukan soji da sauran matakan da ake ɗauka, hare-haren ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya na ci gaba da faruwa. Wannan ya ƙara haifar da damuwa kan yadda za a ci gaba da samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan MNJTF.
-
Ministan Tsaro ya yi kira ga ’yan Najeriya kan imani da haɗin kai
-
Rundunar ’yan sandan birnin tarayya , ta fara neman direban da ya haddasa tashin gobara a Kubwa
A Borno kuwa, Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar ta yi kira ga gwamnatin tarayya, da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙarin ceto ’yan makaranta 78 da aka sace, waɗanda suka shafe sama da kwanaki 100 a hannun masu garkuwa.
Shugaban CAN na Borno, Reverend John Bakeni, ya yi wannan kiran ne a wani taron addu’a da aka gudanar a Maiduguri yayin bikin cika shekaru 50 da kafa ƙungiyar.
Ya ce rashin tsaro ya sa ba a iya gudanar da bukukuwan cikar shekaru yadda aka saba ba.
’Yan makarantar 78 sun haɗa da 42 daga firamire na Mussa da Karamar sakandire, waɗanda aka sace a ranar 16 ga Mayu bayan harin da ake zargin Boko Haram ta kai, da kuma mutun 36 daga makarantar sakandire ta jeka kadawo da wani malami a Lassa, waɗanda aka sace a ranar 29 ga Yuni.
Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce ƙasashen Afirka da ke amfana da ayyukan MNJTF ya kamata su ƙara ɗaukar nauyin kuɗaɗen gudanar da rundunar, maimakon dogaro sosai da taimakon ƙasashen waje.
Musa ya bayyana hakan a wani taron tsaro da Ma’aikatar Tsaro ta Najeriya ta shirya a gefen taron babban makon Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a New York.
Ya ce ya zama dole ƙasashen yankin su mallaki tsarin tsaron nasu ta hanyar samar da kuɗaɗen da suka dace.
A taron kwamitin gudanarwa na MNJTF karo na 18 da aka gudanar a N’Djamena a ranar 7 da 8 ga Satumba, rundunar ta bayyana buƙatar samun ingantattun na’urorin sadarwa, fasahar yaƙi da jirage marasa matuƙa, injinan yaki da kayan gano abubuwan fashewa.
Bayanai da The Guardian ta ruwaito sun nuna cewa Najeriya ta riga ta kashe kusan dala miliyan 209.08 wajen MNJTF tsakanin 2015 zuwa 2021.
Sai dai ba a bayyana cikakken adadin kuɗin da kowace ƙasa mai bayar da sojoji ke bayarwa a yanzu ba.
Haka kuma, Tarayyar Turai ta ce ta bayar da kusan kimanin €234. domin tallafa wa MNJTF, ciki har da kayan aiki, da sufuri, da kiwon lafiya, da leƙen asiri da sa ido.
Birtaniya ma ta samar da £5m, yayin da Tarayyar Afirka ta bayar da $1m daga asusun gaggawa na zaman lafiya a watan Mayun 2026.
Matsalar tsaron ta kuma haifar da ƙaura mai yawa. A cewar bayanan UNHCR da The Guardian ta ambato, adadin abubuwan da suka shafi tsaro a yankin ya ƙaru da kashi 80 cikin 100 tsakanin Janairun 2024 da Afrilun 2026.
A tsakanin Satumban 2025 da Mayun 2026, an samu kusan abubuwan da suka shafi tsaro sama da 1,800 da kuma mutuwar mutane sama da 5,700 a yankin tafkin Chadi.
UNHCR ta ce sama da mutane miliyan 3.5 ne suka rasa matsugunansu a faɗin yankin, yayin da mutane miliyan 8.2 ke buƙatar tallafin jin ƙai.
Tsohon Darakta-Janar na Land Forces Simulation Centre, Manjo Janar Dayo Olukoju mai ritaya, ya ce ya kamata Najeriya ta sake tsara dabarunta bayan dakatar da shigar Nijar cikin MNJTF.
Sai dai masani kan tsaro Kabiru Adamu ya ce bai kamata a ɗora matsalar kuɗin rundunar kacokan kan rashin ƙoƙarin sauran ƙasashe ba, yana mai cewa ana buƙatar tsarin tallafin kuɗi na haɗin gwiwa.
Farfesa Philip Dahida na Jami’ar Abuja shi ma ya ce matsalar ba ta tsaya kan kuɗi kawai ba.
Ya ce ƙasashen yankin na buƙatar ƙara haɗin kan siyasa, tare da magance matsalolin talauci, da rashin aikin yi da rashin samun ilimi, da domin ayyukan soji kaɗai ba za su kawar da tushen matsalar tsaro a yankin tafkin Chadi ba. Ya kuma yi kira da a ƙara bayyana yadda ake amfani da tallafin tsaro daga ƙasashen waje.