A lokacin samun ’yancin kai, babban aikin rundunar tsaron Najeriya shi ne kare ikon ƙasa da iyakokinta. Amma shekaru 66 bayan haka, yanayin tsaron ƙasar ya sauya sosai. A yau, sojoji da sauran hukumomin tsaro ba sa fuskantar barazana daga waje kawai; suna kuma tunkarar ta’addanci, da ’yan bindiga, da  garkuwa da mutane, da satar mai da sauran nau’o’in laifukan da ke barazana ga rayuwar jama’a.

Ma’aikatar Tsaro ta Najeriya, wadda aka kafa tun 1958, ta ce rundunar tsaron ƙasar ta shiga matakai daban-daban tun bayan samun ’yancin kai, ciki har da yaƙe-yaƙe na gargajiya, da ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma sabbin barazanar tsaro da ba su da wata ƙayyadaddiyar fuska. Wannan sauyin ya tilasta ƙasar ta sauya yadda take tsara ayyukan tsaro.

Daga Operation Hadin Kai da ke yaƙi da Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, zuwa Operation Fansan Yamma da ke yaƙi da ’yan bindiga a Arewa maso Yamma, sojojin Najeriya yanzu suna gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a sassa daban-daban na ƙasar. A Neja Delta kuma, Operation Delta Safe na mayar da hankali kan satar mai da kare muhimman ababen more rayuwa, yayin da Operation Whirl Stroke ke aiki a yankin Arewa ta Tsakiya.

Wannan ya nuna cewa tsaron Najeriya ya zama aiki da ya shafi fiye da ƙarfin soja. Haɗin gwiwar Sojoji, da ’Yan Sanda, da NSCDC, da DSS da hukumomin farar hula na ƙara zama muhimmi wajen tattara bayanan sirri, da kare fararen hula da kuma magance matsalolin da ke haddasa rikici.

Ma’aikatar Tsaro ta ce rundunar ƙasar ta kuma shiga sama da ayyukan wanzar da zaman lafiya 40 tun daga 1960, abin da ya nuna cewa Najeriya ta taka rawa wajen tsaro ba a cikin ƙasa kaɗai ba, har ma a Afirka da duniya.

A shekarar 2026, gwamnati ta ƙara mayar da hankali kan sake fasalin tsarin tsaron ƙasar. A cikin kasafin kuɗin 2026, an ware Naira tiriliyan 5.41 ga tsaro da harkokin tsaro, tare da jaddada bukatar inganta kayan aiki, da tattara bayanan sirri, da tsaron iyakoki da ayyukan haɗin gwiwa. Gwamnati ta kuma ce tana ƙoƙarin gina sabon tsarin yaƙi da ta’addanci da sauran laifukan tashin hankali.

Ma’aikatar tsaron Nigeria

Wani sabon mataki kuma shi ne umarnin da aka bayar a watan Agustan 2026 na gudanar da cikakken Binciken Barazanar Tsaro na Ƙasa da kuma tsara wani shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar. Manufar shirin ita ce gano manyan barazanar da ƙasar ke fuskanta, da tantance gibin kayan aiki da ƙarfin rundunoni, sannan a tsara yadda za a rarraba albarkatu bisa bukatun tsaro.

Sai dai shekaru 66 sun kuma nuna cewa ba za a magance matsalar tsaro da ƙarfin makami kaɗai ba. Rashin aikin yi, da talauci, da rikicin manoma da makiyaya, da raunin tsarin shari’a, da fataucin miyagun ƙwayoyi, da matsalar iyakoki da kuma ƙarancin bayanan sirri daga al’umma na iya taimakawa wajen haifar da yanayin da laifuka ke bunƙasa. Shi ya sa haɗin gwiwar gwamnati da al’umma ke da muhimmanci wajen gina zaman lafiya mai ɗorewa.

Ministan tsaro General Christopher Musa

A watan Fabrairun 2026 ma, an buɗe muhawara kan yiwuwar kafa ’yan sandan jihohi, inda gwamnati ta ce tsarin zai iya ƙara ƙarfafa tsaron al’umma da saurin mayar da martani ga barazanar da ke faruwa a matakin ƙananan hukumomi da jihohi. Wannan na daga cikin muhawarar da ke nuna cewa tsarin tsaron Najeriya yana ci gaba da neman sabuwar hanya da ta dace da irin barazanar da ƙasar ke fuskanta a yanzu.

Don haka, bayan shekaru 66, tambayar da ta fi muhimmanci ba ita ce ko Najeriya tana da rundunar tsaro mai ƙarfi ba. Tambayar ita ce ko ɗan ƙasa zai iya noma, da kasuwanci, da tafiya zuwa aiki, da zuwa makaranta da gudanar da rayuwarsa ba tare da tsoron hare-hare, ko garkuwa da mutane ko sauran laifukan tashin hankali ba.

Tsaron da ake so a Najeriya a shekaru masu zuwa shi ne wanda zai wuce nasarar da ake samu a fagen yaƙi, ya koma zaman lafiya mai ɗorewa, da kariyar rayuka da dukiyoyi, da samar da yanayin da tattalin arziki da al’umma za su iya bunƙasa. Wannan ne zai nuna a aikace cewa shekaru 66 na ƙasar sun haifar da tsaro da zai amfani ɗan Najeriya a rayuwarsa ta yau da kullum.

 

 

 

 

 

 

 

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *