Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ziyarci matatar man Azikel da ke Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda ya duba yadda aikin gina matatar ke gudana.
Jonathan ya yaba wa shugaban kamfanin Azikel Group, Dr Eruani Azibapu, bisa ƙoƙarinsa na ƙara bunƙasa tace danyen mai a cikin gida, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na taimakawa wajen ƙarfafa dogaro da kai da samar da makamashi a Najeriya.
- NAF ta kammala sake haɗa jirage masu saukar ungulu biyu a Lagos
- Tinubu ya bar Paris, zai dawo Najeriya
Ya ce matatar Azikel, tare da wasu manyan ayyukan kamfanoni masu zaman kansu kamar matatar Dangote, na da muhimmiyar rawa wajen ƙara yawan man da ake tacewa a cikin ƙasa da kuma rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yi fatan samun nasarar kammala aikin, tare da bayyana fatansa cewa matatar za ta taimaka wajen ƙara yawan man fetur da ake samarwa a cikin gida domin biyan buƙatun ’yan Najeriya.
Ya ce ƙara zuba jari a fannin tace mai da sauran ayyukan makamashi na cikin gida na da muhimmanci wajen inganta tattalin arziki da samar da wadataccen makamashi a ƙasar.
[…] Goodluck Jonathan ya yaba da aikin matatar Azikel a Bayelsa […]