Jam’iyyar APC, ta bayar da tallafin Naira miliyan 52 ga iyalan ’yan hakar ma’adinai 37 da suka mutu a hannun Hukumar NSCDC a Jihar Niger, da kuma wasu daga cikin mutanen da suka tsira daga lamarin.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya jagoranci tawagar Kwamitin Aiki na Ƙasa, NWC, zuwa gidan gwamnatin Jihar Niger da ke Minna, domin jajanta wa Gwamna Umaru Bago da al’ummar jihar kan lamarin.
Gwamna Umaru Bago ya ce Yilwatda ya bayar da Naira miliyan ɗaya ga kowane daga cikin iyalan mutane 37 da suka mutu, wanda ya kai Naira miliyan 37, yayin da aka ware Naira dubu 500 ga mutanen da aka kama tare da raunata a yayin lamarin.
- Zaman lafiya da tsaro: Nauyin kowane ɗan ƙasa ne — Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da rajistar matasa masu shekaru 15 zuwa 35
- Tinubu ya dawo Najeriya bayan kwana 30 baya ƙasar
Gwamnan ya bayyana cewa za a raba tallafin ne ta wani kwamiti da mataimakinsa Yakubu Garba ke jagoranta, tare da haɗin gwiwar Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago, domin tabbatar da cewa ya isa ga waɗanda abin ya shafa.
A yayin ziyarar, Yilwatda ya bayyana mutuwar mutanen a matsayin wani lamari mai cike da baƙin ciki, tare da mika ta’aziyyar jam’iyyar ga gwamnati da al’ummar Jihar Niger.
Ya kuma nuna goyon bayan jam’iyyar ga gwamnatin jihar a wannan lokaci, tare da bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da jihar ke fuskantar wasu ƙalubalen tsaro.
Bago ya ce har yanzu yanayin da ya kai ga mutuwar mutanen na ci gaba da jawo damuwa, yana mai cewa kwamitocin da aka kafa domin gudanar da bincike suna aiki don gano abin da ya faru.
Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti mai mutane 10 domin gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutuwar ’yan hakar ma’adinan, tare da neman gano abin da ya faru da kuma tantance alhakin waɗanda bincike ya nuna suna da hannu.
Bayan ziyarar gidan gwamnati, shugaban APC na ƙasa da tawagarsa sun kuma kai ziyara fadar Sarkin Minna domin jajanta wa masarautar kan mutuwar mutanen.
Lamarin dai na ci gaba da jan hankali, yayin da iyalan waɗanda suka mutu ke jiran sakamakon binciken da gwamnati ta kafa domin gano musabbabin mutuwar ’yan hakar ma’adinan.