Yadda hanyar Abuja zuwa Kaduna ta kasance[Aliyu Ibrahim Makama]

Daruruwan mutane ne suka yi cirko-cirko a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, sakamakon cunkoson ababen hawa daya takaita zirga zirgar mutane a hanyar.

Rahotanni sun bayyana cewa cunkoson ya afkune sakamakon lalacewar wata babbar mota akan hanyar, a dai dai lokacin da al’umma da dama ke komawa jihohin dake kan babbar hanyar domin bukukuwan babbar Sallah.

Fasinjoji da dama sun shaidawa wakilin mu Binyaminu Bello damuwar su kan yadda cunkoson ya jawo musu tsaikon isa garuruwan su akan lokaci.

Yayinda wasu Direbobin manyan motocin dakon kaya  ke bayyana cewa sun kwashe kwanaki biyu a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rahotanni na nuni da cewa a duk shekara akan samu irin wannan cunkoson ababen hawa akan hanyar, sakamakon karuwar matafiya don gudanar da bukukuwan sallah.

Wani abu daya Kara haifar da cunkoson shine, tsawon da gyaran hanyar ya shafe anayi ba tare da kammalawa ba, wanda ya zamewa Direbobi dole bin hannu daya.

Sai dai tunda sanyin safiya hukumar kiyaye aukuwar haddura ta kasa (FRSC) ta shawarci wadanda ke shirin bin hanyar da suyi anfani da wata karamar hanya da ta tashi  daga Bwari zuwa Kachia, domin kaucewa cun koson.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *