Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, kan ikirarin da ya yi cewa tsadar magunguna sakamakon manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta taka rawa wajen rasuwar mahaifiyarsa.

Amaechi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce tsadar magunguna a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu ta sa ya fuskanci wahalar samun magungunan da mahaifiyarsa ke buƙata.

Sai dai Wike ya soki Amaechi kan shigar da batun rasuwar mahaifiyarsa cikin siyasa, yana tambayar yadda tsohon minista kuma tsohon gwamnan jihar zai ce ya kasa samun kuɗin sayen magungunan mahaifiyarsa.

Wike ya kuma yi ishara da gidajen da ya ce Amaechi yana da su a Old GRA da Abuja, yana mai tambayar dalilin da ya sa bai nemi taimakon abokansa da sauran makusantansa ba idan da gaske yana fuskantar matsalar kuɗi.

A yayin wani taro da shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a Ahoada, Rivers, Wike ya ce ya yi matuƙar takaicin yadda aka kawo batun mahaifiya cikin muhawarar siyasa, inda ya furta cewa gara mutum ya zauna ba tare da ɗa ba fiye da samun ɗa mai yin irin wannan magana.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *