Tawagar ƙwallon ƙafa ta guragu ta maza ta Najeriya, wato Special Eagles, na ƙara zage damtse a atisaye a Abuja, gabanin halartar Gasar Cin Kofin Duniya ta guragu ta 2026.
Ƙasar Mexico ce za ta karɓi bakuncin gasar ta bana, daga ranar 13 zuwa 22 ga Nuwamba a San Juan De Los Lagos.
Kyaftin din Special Eagles, Sarafadeen Olalekan Oyeleke, ya ce ‘yan wasan suna ba da dukkan ƙoƙarinsu a atisaye don shirya wa gasar, tare da samun goyon baya daga Hukumar Wasanni ta Kasa da kuma Hukumar Kwallon Kafa ta Guragu ta Najeriya.
-
Fury ya gayyaci Trump zuwa kallon karawar sa da Joshua
-
Yadda Senegal ta doke Sand Eagles a wasan sada zumunta a Kaduna
-
Najeriya za ta kara a rukunin A na Gasar Cin Kofin Duniya
Najeriya na daga cikin tawagar Afirka guda bakwai da za su fafata a Gasar Cin Kofin Duniya, tare da Laberiya, Aljeriya, Masar, Angola, Ghana da Maroko.
Gaba ɗaya, ƙungiyoyi 24 ne za su fafata don neman lashe kambun duniya.
An gudanar da rabe-raben rukuni a ranar 26 ga Satumba, inda mai masaukin baki Mexico ta fada a rukuni na A tare da Italiya, Laberiya da Aljeriya.
-
Fury ya gayyaci Trump zuwa kallon karawar sa da Joshua
-
Yadda Senegal ta doke Sand Eagles a wasan sada zumunta a Kaduna
-
Najeriya za ta kara a rukunin A na Gasar Cin Kofin Duniya
Kasar Turkiyya, da Spaniya, da kuma Masar za su fafata da Najeriya a rukuni na B.
Yayin da Brazil, da Jamus da Japan za su yi fafatawa a rukuni na C.
Rukuni na D ya kunshi Angola, Ghana, Colombia da Iraq.
Rukuni na E na da Uzbekistan, Maroko, Amurka da Uruguay.
Yayin da Ingila, Poland, Iran da Costa Rica za su fafata da juna a rukuni na F.
Ana gudanar da gasar duk bayan shekaru hudu, kuma an fara gunadar da wasan ne tun 1986.
Rasha da Uzbekistan ne suka fi samun nasarar lashe gasar da kofuna 5 kowacce, sai Brazil, Ingila da El Salvador da ke da kofi uku kowacce.
Angola ta zama tawagar Afirka ta farko da ta lashe kofin duniya na kwallon kafa na guragu a 2018 ta hanyar doke Turkiyya. Sai dai a 2022, al’amura sun sauya yayin da Turkiyya ta doke Angola ta dauki kofin.