Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta ce ambaliyar ruwa ta shafi al’ummomi shida da sansanin ‘yan gudun hijira guda a yankin Kukareta da kewaye, cikin ƙaramar hukumar Damaturu.
SEMA ta ce gidaje 143 da ke ɗauke da mutane 1,020 ne abin ya shafa, yayin da matsugunai 278 suka lalace.
Hukumar ta ce sansanin ‘yan gudun hijira na Kokari ne ya fi fuskantar matsalar, inda gidaje 48 suka shiga cikin lamarin.
- APC ta caccaki Amaechi kan zargin kasa biyan maganin mahaifiyarsa
- An kashe mutane uku a Minna sakamakon zanga-zangar ‘yan daba a jihar
Sai dai hukumar ta ce babu asarar rai ko jikkata da aka samu, kuma babu wani ginin gwamnati da ya lalace.
SEMA ta shawarci mazauna yankunan da su kasance cikin shiri, su nisanci wuraren da ruwa ya mamaye, tare da kula da tsaftar ruwan sha domin kauce wa cututtukan da ruwa ke yaɗawa.
Hukumar ta ce tana haɗa kai da sauran hukumomi da abokan hulɗa domin samar da agajin gaggawa, musamman ga sansanin Kokari da iyalan da ambaliyar ta fi shafa.