Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya nemi ’yan Najeriya su ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa manufofin gwamnatin na mayar da hankali ne kan magance manyan ƙalubalen ƙasar da kuma bunƙasa rayuwar jama’a.
- Jigawa ta ƙara kasafin kuɗi da Naira biliyan 63.4 domin ayyukan ci gaba
- Kaduna ta shafe sama da shekaru uku ba tare da rikicin ƙabilanci ko addini ba – Uba Sani
Uzodimma ya bayyana hakan ne bayan halartar taron APC Women Stakeholders’ Mobilisation and Empowerment Pre-Inaugural Summit, wanda aka gudanar a Bola Ahmed Tinubu International Conference Center (BATICC).
Ya ce jam’iyyar APC na ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya gabanin zaɓen 2027, tare da yin kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin Tinubu baya domin tabbatar da abin da ya kira ci gaba da sauyin ƙasa.