Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilin da ya sa ya bar sansanin tawagar Portugal, yana mai cewa kocin ƙungiyar, Jorge Jesus, ya karya alkawarin da suka yi tsakaninsu.
Ronaldo ya ce tun farko sun tsara cewa zai buga wasan farko da na ƙarshe na wasannin, domin kula da lafiyarsa. Sai dai a ranar wasan da Norway, kocin ya sanar da shi cewa zai buga mintuna 30.
Ronaldo ya ce ya yi atisaye domin shiga wasan, amma daga baya ba a saka shi ba.
- Kwamishinan ’yan sandan Ondo ya ziyarci wurin haɗarin Igbokoda
- ICRC ta ƙaddamar da taron ƙwararru kan batun mutanen da suka ɓace
Ya ce abin ya ba shi mamaki, domin ya riga ya amince da tsarin da aka tsara masa. “Kocin ya karya alkawarinsa da ni,” in ji Ronaldo a cikin bayanin da ya fitar.
Ronaldo ya kuma ce daga baya an sake samun wata yarjejeniya kan yadda za a bayyana lamarin a bainar jama’a, amma ya yi zargin cewa bayanan da kocin ya bayar ba su yi daidai da abin da suka amince a kansa ba.
Duk da rikicin, Ronaldo ya nemi afuwar magoya bayan Portugal da abokan wasansa kan yadda ya bar sansanin, kuma ya ce a shirye yake ya karɓi duk wani hukunci da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Portugal za ta ɗauka a kansa.
Ya kuma jaddada cewa bai yi ritaya daga buga wa Portugal wasa ba, yana mai cewa idan yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana taka rawar gani a kulob dinsa, zai kasance a shirye ya sake wakiltar ƙasarsa.