Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na gaggauta samar da Dokar Kula da Abinci da Gina Jiki ta Ƙasa, domin kare kuɗaɗen da ake warewa harkokin abinci da gina jiki, ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma tabbatar da dorewar shirye-shiryen kula da abinci mai gina jiki a gwamnatoci daban-daban.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin taron Musayar Ra’ayoyin Shugabanni kan Gina Jiki tsakanin Najeriya da Habasha da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Ya ce samar da dokar zai ƙarfafa shirin gwamnatin tarayya na Shirin Gina Jiki na Ƙasa a kananan hukumomi 774, tare da zurfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi wajen yaƙi da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Mataimakin shugaban ƙasan ya ce Manufar Ƙasa kan Abinci da Gina Jiki ta 2026–2035 na da burin rage yawan yara masu fama da matsalar ƙarancin girma sakamakon rashin abinci mai gina jiki daga matakin da ake ciki zuwa kashi 32 cikin 100 nan da shekarar 2029, kashi 28 cikin 100 zuwa 2032, da kuma kashi 25 cikin 100 zuwa 2035.

Ya kuma bayyana cewa gudunmawar Najeriya ta dala miliyan 26 ga Asusun Kula da Gina Jikin Yara ta jawo ƙarin tallafin da ya kai dala miliyan 26, wanda ya sa jimillar kuɗin da aka samu ta kai dala miliyan 52.

Ya ce tun daga shekarar 2023, jihohi 21 sun bayar da gudunmawar dala miliyan 6.3 domin taimakawa wajen dakile da kuma magance matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Shettima ya kuma bayyana cewa Asusun Zuba Jari na Shugaban Ƙasa kan Gina Jiki da ake shirin samarwa zai taimaka wajen samar da kuɗaɗen da za su fara aiwatar da muhimman shirye-shirye, yayin da gwamnati ke ci gaba da ƙarfafa tsarin da zai haɗa kuɗaɗen da ake kashewa daga baitulmalin gwamnati da sakamakon da za a iya auna wa a fannin inganta abinci da gina jiki.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *