Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki ta EFCC reshen Kano ta ce za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai domin yaƙi da laifukan tattalin arziki da kuɗi.
Daraktan shiyya na EFCC a Kano, Assistant Commander of the EFCC, ACE1 Friday S. Ebelo, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi Shugaban Kamfanin Matashiya TV, Abubakar Murtala Ibrahim, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa da ke Kano ranar Laraba.
Ebelo, wanda ya yi magana a madadin Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce kafafen yaɗa labarai na daga cikin manyan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da nasarar aikin hukumar, musamman wajen wayar da kan jama’a da hana aikata laifukan kuɗi.
- NLC ta fara yajin aikin sai abinda hali ya yi a Abuja kan rikicin malamai
- INEC ta ce ba za a bar masu kaɗa ƙuri’a a baya
- Shettima ya ce za a gaggauta samar da dokar abinci da gina jiki
Ya ce aikin EFCC ya haɗa da yaƙi da damfara, laifukan yanar gizo, safarar kuɗaɗen haram, cin hanci da rashawa a hukumomin gwamnati da sauran laifukan da ke cutar da tattalin arzikin ƙasa.
A nasa ɓangaren, Shugaban Matashiya TV, Abubakar Murtala Ibrahim, ya ce kafar na da shirye-shiryen wayar da kan matasa domin rage shiga laifukan yanar gizo da tashin hankali.
Ya ce Matashiya TV ta horar da matasa sama da 3,000 kan sana’o’i da dabarun dogaro da kai.
Ya ce kafa dangantaka mai ɗorewa da EFCC za ta taimaka wajen samar da shirye-shiryen da za su ƙara wayar da kan al’umma kan illolin laifukan tattalin arziki da hanyoyin da za a guje musu.
Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin EFCC da Matashiya TV domin tallafa wa yaƙi da laifukan tattalin arziki da kuɗi a Kano da sauran sassan ƙasar.