Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da almundahana da dukiyar gwamnati, tare da gargaɗin cewa zai iya fuskantar matsala wajen gudanar da kamfen a jihar Ribas idan ya ci gaba da amfani da kalaman cin zarafi ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da magoya bayansa.
Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman Amaechi, wanda yake cikin masu fafutukar neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
Ya kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro da su ɗauki mataki kan ’yan siyasar da ke amfani da kalaman da ka iya tunzura jama’a a lokacin kamfen.
- TUC ta umarci mambobinta su yi watsi da yajin aikin NLC a Abuja
- Gwamnatin tarayya ta saki alawus ga manyan ma’aikatan jamio’i
- FCC ta jaddada muhimmancin ingantattun ƙididdiga wajen tabbatar da adalci a wakilcin tarayya
Ministan ya zargi Amaechi da bayyana cewa barayi ne kawai za su zaɓi Tinubu, tare da cewa mahaukata ne kawai za su zaɓe shi.
Wike ya ce irin waɗannan kalamai ba su dace da mutumin da ke neman shugabancin ƙasa ba, yana mai cewa ya kamata ’yan siyasa su mayar da hankali kan manufofinsu da abubuwan da za su yi wa jama’a idan aka zaɓe su.
Wike ya kuma zargi kafafen yaɗa labarai da kasa yin tambayoyi masu zurfi kan wasu ayyuka da kuɗaɗen da ake zargin an kashe a lokacin da Amaechi yake gwamnan jihar Ribas.
Ya yi tambaya kan wani aikin gina asibitin da ake kira Caribbean White House, wanda ya ce an yi iƙirarin kashe dala miliyan 39 wajen gudanar da shi, amma har yanzu ba a ga aikin ba.
Haka kuma, ya yi tambaya kan dala miliyan 10 da ya ce an kashe wajen fesa maganin sauro a jihar, yana mai cewa har yanzu mazauna jihar na fama da cizon sauro.
Wike ya yi gargaɗin cewa magoya bayansa ba za su amince da duk wani yunƙuri na cin zarafin shugaban ƙasa ko tunzura jama’a a jihar Ribas ba.
Ya ce ya kamata ’yan siyasa su gudanar da kamfen cikin mutunci, su bayyana manufofinsu da shirye-shiryensu maimakon zagin abokan hamayya.