NFF tace dole ne wadanda zasu samu horon su cika dukkanin sharuddan data gindaya

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta sanar da bude shirye-shiryen horar da masu horas wa a Abuja.

A wani sako da ta wallafa a shafin ta na Intanet, (NFF) ta ce horon zai shafi matakai biyu na samun kwarewar ta lasisin CAF “A”, sai kuma bangaren ilmi mai zurfi da aka yi wa lakabi da CAF “B” da zai kai ga samun babban matsayi.

Rukunan an tsara su ne domin bunkasa kwarewa da zurfafa ilimi da dabaru na masu horar da ‘yan wasan kwallon kafa a fadin Najeriya.

Cikin sharuddan da NFF ta gindaya dole ne mai horarwa ya zamanto yana koyar wa a matakin Kungiyoyin Kasa.

Sannan yana da takardar shaidar Diploma ta CAF “A” ta kasashen waje da aka amince da ita, ko kuma Diploma ta CAF “B” , kuma yayi aiki da hukumar aƙalla shekaru Biyu zuwa Uku.

Haka nan sanarwar tace dole wanda zai samu horon ya zamanto kwararre a Harshen Turanci a fannin karatu da rubutu, da ilmin na’ura mai kwakwalwa.

NFF tace gurabe 25 ne kacal za ta dauka a rukunin karshe na shirin, kuma zata gudanar da gwaji ga wadanda suka yi nasara ta kafar intanet, kafin gabatar da kansu gabanta daga ranar 1 zuwa 23 ga watan Yuni.

Sai Kwas na CAF “B” da za ta gudanar daga ranar 20 zuwa 24 ga Yuni, 2026 a Abuja.

Wadanda zasu samu horo akan Lasisin CAF “A” zasu kwashi watanni bakwai, wanda za a raba gida shida daga ranar 2 ga watan Agusta 2026 zuwa 7 ga watan Fabarairun shekarar 2027 a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *