Dakarun sojojin Najeriya mai tabbatar da zaman mai dorewa ta Operation Enduring Peace sun kama mutum huɗu da ake zargi da ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma safarar bindigogi a ƙananan hukumomin Mangu da Barkin Ladi na Jihar Filato.

A yayin samamen, dakarun sun kwato bindigogi da harsasai da wasu kayayyaki da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan safarar makamai, a wani mataki da rundunar ta ce yana da nufin tarwatsa hanyoyin samar da makamai ga masu aikata laifuka a jihar.

Sanarwar rundunar ta bayyana cewa an kai samamen ne tsakanin ranakun 7 zuwa 11 ga Oktoba, 2026, bayan samun bayanan sirri a ranar 4 ga Oktoba.

Dakarun sassa na 8 da na 4 ne suka aiwatar da samamen a wurare daban-daban na ƙananan hukumomin biyu.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindiga da aka ƙera a gida, bindigar hannu, bindigar AK-47, da harsasai 42 masu girman 7.62 x 54mm, tare da wasu kayayyaki da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan.

Sanarwar ta kuma ce bayanan farko da aka samu yayin tambayoyin da aka yi wa waɗanda ake zargin sun nuna zargin cewa an sayi harsasan da aka kwato kan naira 3,000 kowanne daga wani sojan da ba a bayyana sunansa ba.

Sai dai rundunar ta jaddada cewa har yanzu ba a tabbatar da wannan zargi ba, kuma ana gudanar da bincike domin gano sahihancinsa da duk wanda ka iya kasancewa yana da hannu a lamarin.

A halin yanzu, waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato suna hannun hedikwatar Operation Enduring Peace domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

Rundunar ta ce tana kuma ƙara zurfafa bincike da gudanar da wasu samame domin gano sauran mutanen da ake zargin suna da hannu a hanyar samar da makaman.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ayyukan na daga cikin ƙoƙarinta na dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma tarwatsa hanyoyin ayyukan masu aikata laifuka.

Ta kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *