Lauyoyin Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, sun ba Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wa’adin kwanaki uku domin ta saka sunansa cikin jerin ’yan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.

Lauyoyin sun bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 12 ga Oktoba, 2026, wadda aka aika wa shugaban INEC.

A wasiƙar, sun buƙaci hukumar ta wallafa sunan Pantami kafin ko a ranar Laraba, 14 ga Oktoba, 2026, tare da ba shi irin matsayin da sauran ’yan takarar da aka wallafa sunayensu suka samu.

Sun bayyana cewa cire sunan Pantami daga jerin ’yan takarar da INEC ta wallafa a ranar 10 ga Oktoba, 2026, bai dace da doka ba, musamman ganin cewa hukumar ta wallafa sunansa a jerin wucin gadi a ranar 29 ga Agusta, 2026.

A cewar lauyoyin, Pantami ɗan jam’iyyar PDP ne mai rajista a mazabar Pantami da ke Jihar Gombe, kuma jam’iyyar ta miƙa wa INEC kundin rajistar mambobinta da ke ɗauke da sunansa.

Sun ƙara da cewa Pantami ya sayi fom ɗin neman takarar gwamna, ya bi tsarin tantance ’yan takara, sannan ya lashe zaɓen fitar da gwani na PDP da aka gudanar a ranar 26 ga Mayu, 2026.

Sai dai, an ƙalubalanci zaɓen a Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe, inda kotun ta soke shi a ranar 24 ga Satumba, 2026 saboda matsalolin da suka shafi yadda aka gudanar da zaɓen.

Kotun ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani cikin kwanaki 30, tare da bai wa waɗanda suka cika sharuddan shiga zaɓen damar sake fafatawa.

Lauyoyin sun ce PDP ta bi umarnin kotun, inda ta gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani a ranar 29 ga Satumba, 2026, wanda jami’an INEC suka halarta tare da sa ido kan yadda aka gudanar da shi.

Sun bayyana cewa Pantami ya sake yin nasara a wannan zaɓe, sannan jam’iyyar ta sake miƙa sunansa ga hukumar a matsayin ɗan takararta.

Sai dai har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, ba a samu martanin INEC kan ƙorafin ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *