Dakarun Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ’yan ta’adda shida da ake zargin ’yan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne, tare da kwato makamai da harsasai bayan dakile wani hari da aka kai sansaninsu na Garaha, a ƙaramar hukumar Hong ta Jihar Adamawa.

A cewar sanarwar rundunar Operation Hadin Kai da ta fitar ranar 13 ga Oktoba, 2026, maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9:07 na dare, inda suka yi ƙoƙarin mamaye sansanin sojojin. Sai dai rundunar ta ce dakarunta sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya.

Sanarwar ta bayyana cewa bayan dakile harin, sojojin sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano gawarwakin ’yan ta’adda shida.

Haka kuma, sun kwato bindiga kirar PKT guda ɗaya da harsasai 67, da bindigogin AK-47 guda shida.

Sauran kayayyakin da aka kwato sun haɗa da harsasai 157 masu girman 7.62mm NATO, da harsasai 120 na 7.62mm Special da kuma bam ɗin turmi mai girman 60mm. Dakarun sun kuma kwato wayar Android ta Infinix, da na’urar ɗaukar bidiyo ta Canon, da jakunkunan ɗaukar ruwa guda uku da wasu kayayyakin yaƙi.

Rundunar ta tabbatar da cewa wasu sojoji sun jikkata yayin arangamar, inda ta ce ana ba su kulawar lafiya tare da shirye-shiryen kwashe su zuwa wuraren da suka dace domin samun ƙarin kulawa.

Ta ƙara da cewa dakarunta na ci gaba da sintiri da binciken yankin domin hana sake kai hare-hare da kuma gano wasu kayayyakin da za su taimaka wajen gudanar da bincike.

Rundunar Operation Hadin Kai ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri domin dakile ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, da kare al’ummomin da ke fuskantar barazanar hare-hare a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *