Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Jihar Kaduna ranar Talata domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin rashawa, tare da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar ADC, Isa Ashiru.
El-Rufai ya isa kotun da misalin ƙarfe 11:50 na safe, gabanin lokacin sauraron shari’ar da aka tsara da ƙarfe 12 na rana, yayin da jami’an tsaro suka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun.
Zuwansa kotun ya biyo bayan umarnin Mai Shari’a Darius Khobo ga Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifukan da suka Shafi Hakan (ICPC), na tabbatar da cewa an gurfanar da shi a gaban kotun domin ci gaba da shari’ar.
- Dangote Cement ta tallafa wa ɗalibai, manoma da ’yan kasuwar Jakura
- Hukumar Shige da Fice ta Gambia ta ceto mutane 111 da ke ƙoƙarin yin ƙaura ta ruwa
An ɗage sauraron shari’ar ranar Litinin bayan El-Rufai bai bayyana a kotu ba. An shaida wa kotun cewa ya nemi ganin likitansa domin duba sakamakon gwaje-gwajen lafiya.
Lauyan masu gabatar da ƙara, Ayodeji Adedipe, ya ce hukumar ICPC ta sanar da shi cewa tsohon gwamnan ya nemi a ba shi damar ganin likitansa. Daga bisani, Mai Shari’a Khobo ya ba da umarnin a kawo shi kotu ranar Talata.
Wannan ya zo ne kwanaki bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna ta yi watsi da ƙarar da El-Rufai ya shigar yana ƙalubalantar ƙin bayar da belinsa.
A hukuncin da ta yanke ranar 9 ga Oktoba, kotun ta tabbatar da matakin babbar kotun, tana mai cewa bai gabatar da isassun dalilan sauya hukuncin ba.
El-Rufai na tsare a hannun ICPC tun ranar 18 ga Fabrairu, 2026, bisa zarge-zargen almundahana da suka shafi yadda ya gudanar da mulkin Kaduna daga 2015 zuwa 2023.
Yana fuskantar shari’o’i daban-daban kan zarge-zargen safarar kuɗaɗen haram, amfani da ofis ta hanyar da ba ta dace ba, zamba da sauran laifukan kuɗi.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa da su, kuma ya bayyana a gaban kotu cewa bai amsa laifinsa ba.