Hukumar Shige da Fice ta Gambia ta ce ta ceto mutane 111 da ke ƙoƙarin yin ƙaura ta ruwa, bayan kwale-kwalensu ya makale a cikin ruwa mai laka a ƙauyen Aljamdu.

Hukumar ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 11 ga Oktoba, 2026, inda jami’anta daga sassan kula da ƙaura da sintirin kan iyaka na Barra suka gudanar da aikin ceton tare da haɗin gwiwar Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa, da Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Gambia, da mazauna ƙauyen.

Mutanen da aka ceto sun haɗa da ’yan ƙasar Guinea 75, Senegal 15, Ivory Coast 10, Saliyo 5, Gambia 4, Mali 1 da Ghana 1.

Hukumar ta bayyana cewa cikin mutanen akwai maza 58 da mata 53, ciki har da ƙananan yara 12.

A halin yanzu, an kai mutanen ofishin hukumar da ke Barra domin tantance bayanansu da gudanar da ƙarin bincike.

Hukumar ta ce aikin ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, al’ummomin yankuna da abokan hulɗa na ƙasashen duniya wajen tunkarar ƙaura ba bisa ƙa’ida ba da inganta tsarin kula da masu ƙaura.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *