’Yan takarar jam’iyyar PDP guda uku da ke neman kujerun Majalisar Dokokin Tarayya a Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) sun janye takararsu, tare da goyon bayan ’yan takarar jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.

’Yan takarar da suka janye su ne Gomna Stephen Gashe, mai neman kujerar wakiltar Abaji, Gwagwalada, Kwali da Kuje; Ahmed Dogara Jacob, mai neman kujerar Municipal da Bwari; da Angulu Bako, wanda ke neman kujerar Sanata.

Sun sanar da matakin ne ranar Litinin a Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar Rainbow Coalition, wadda Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kira domin haɗa kan ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban wajen tallafa wa sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

’Yan takarar APC da za su amfana da matakin sun haɗa da Danladi Chiya, mai neman kujerar Abaji, Gwagwalada, Kwali da Kuje; Shekwogaza Gabaya, mai neman kujerar Municipal da Bwari; da Philip Aduda, wanda ke neman kujerar Sanata.

Da yake jawabi a taron, Wike ya ce ya amince a bar wa APC kujerun Majalisar Dokokin Tarayya na FCT saboda Shugaba Tinubu na zaune a yankin.

Ya bayyana kansa a matsayin jagoran siyasa na sake zaɓen Tinubu a FCT da Jihar Rivers.

Wike ya ce duk da bambancin jam’iyyunsu, ya kamata ’yan siyasar PDP da APC su haɗa kai wajen cimma burin sake zaɓen shugaban ƙasar.

Ya kuma ce a jiharsa ta Rivers, yana fatan samun wasu kujeru, duk da cewa ya amince a bar wa APC kujerun uku na FCT.

Bayan haka, ’yan takarar PDP ɗin sun bayyana goyon bayansu ga Wike tare da alƙawarin yin aiki tare da shi.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC kan ƙungiyar Rainbow Coalition.

Gwamnonin sun bayyana cewa ba za su goyi bayan wata ƙawance ko tsarin siyasa da zai iya raunana APC ko kawo cikas ga sake zaɓen Tinubu a 2027 ba.

Sun kuma yi gargaɗin cewa ba za su amince da duk wani tsari da zai haifar da ruɗani, ko rabuwar kai ko saɓanin biyayya a cikin APC ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *