Kwamishinan ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja (FCT), CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya karɓi baƙuncin Kwamandan rundunar tsaron hedikwatar tsaro ta sojin Najeriya, Manjo Janar RT Utsaha, a ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Abuja.

Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce ziyarar ta gudana ne a ranar Talata, 13 ga Oktoba, 2026.

A yayin ganawar, jami’an sun tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin rundunar ’yan sandan FCT da rundunar tsaron hedikwatar tsaro ta sojin Najeriya, musamman wajen musayar bayanan sirri, gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da kuma ci gaba da haɗa kai domin inganta tsaro a babban birnin tarayyar.

Kwamishinan ’yan sandan ya gode wa Manjo Janar Utsaha da tawagarsa bisa ziyarar, tare da jaddada aniyar rundunarsa na ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, musamman sojoji, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna FCT.

Sanarwar ta ƙara da cewa ziyarar ta ƙare ne da musayar fatan alheri tsakanin jami’an biyu da kuma ɗaukar hoton haɗin gwiwa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *