Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta ce ta ƙara ƙaimi wajen neman tarkacen jirginta da gudanar da aikin ceto bayan hatsarin jirgin ATR 42 mai lamba NAF 931, wanda ya faru a Igbokoda, Jihar Ondo, ranar 5 ga Oktoba, 2026.
Rundunar ta kuma sanar da kafa kwamitin ƙwararru mai mutum 12 domin binciken musabbabin hatsarin, gano abubuwan da suka haddasa shi da kuma ba da shawarwarin da za su taimaka wajen hana sake faruwar irin wannan lamarin.
Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ne ya bayar da umarnin ci gaba da aikin bincike da ceto.
- APC ta ce ba za ta yi koyi da yadda Atiku ke kiran Tinubu da sunansa ba
- El-Rufai ya gurfana a kotu domin ci gaba da shari’ar rashawa
Kwamitin, wanda Air Vice Marshal FO Ankeli ke jagoranta, ya ƙunshi ƙwararru a fannin zirga-zirgar jiragen sama, da kiyaye lafiyar jiragen, tukin jirgi, kula da zirga-zirgar jiragen sama, injiniyanci, gyaran jirage da ayyukan lafiya.
Haka kuma, akwai wakilai daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da Hukumar Binciken Haɗurra ta Najeriya (NSIB).
Rundunar ta ce kwamitin zai binciki abubuwan da suka shafi aikin jirgin, fasaha, yanayin wurin, kuskuren ɗan Adam da tsarin gudanarwa da ka iya taimakawa wajen faruwar hatsarin.
Za a kuma tantance yadda aka gudanar da aikin gaggawa, da neman waɗanda suka ɓace, da ceto da kula da wurin da hatsarin ya faru.
A wani ɓangare kuma, rundunar ta ce ta buɗe layin waya na musamman a hedikwatarta, ƙarƙashin ofishin Daraktan Kula da Tsofaffin Ma’aikata, domin bai wa iyalan waɗanda abin ya shafa damar samun bayanai da amsoshin tambayoyinsu.
Ta kuma ce ta fara shirye-shiryen gudanar da tarurruka da iyalan domin ba su tallafi da taimako a wannan lokaci na alhini.
Rundunar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da tabbatar da cewa za ta sanar da jama’a bayanan da aka tantance yayin da ake ci gaba da bincike.