Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki ta Najeriya (EFCC), tare da haɗin gwiwar rundunar ’yan sandan Koriya ta Kudu, sun ƙaddamar da shirin horas da jami’ai na tsawon kwanaki 10 kan gano kadarorin da aka samu ta haramtacciyar hanya da binciken laifukan da suka shafi kuɗaɗen intanet (cryptocurrency).
Shirin horaswar da aka fara ranar Talata, 13 ga Oktoba, 2026, a Cibiyar Horar da Jami’an EFCC da ke Karu, Abuja, ya haɗa jami’an bincike sama da 30 na hukumar domin ƙara musu ƙwarewa wajen yaƙi da sabbin dabarun aikata laifukan kuɗi.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, wanda mukaddashin shugaban cibiyar horas da jami’an hukumar, ACE1 Joseph Ogwiji, ya wakilta, ya ce ƙaruwa da amfani da fasahohin hada-hadar kuɗi ta intanet da kadarorin dijital na buƙatar jami’an bincike su ci gaba da sabunta iliminsu da ƙwarewarsu.
- APC ta ce ba za ta yi koyi da yadda Atiku ke kiran Tinubu da sunansa ba
- Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kafa kwamitin binciken hatsarin jirginta a Ondo
- El-Rufai ya gurfana a kotu domin ci gaba da shari’ar rashawa
Ya ce duk da amfanin waɗannan fasahohi ga tattalin arziki, masu laifi na iya amfani da su wajen damfara, da tura kuɗaɗen haram da ɓoye ainihin waɗanda ke aikata laifuka.
Olukoyede ya jaddada cewa, saboda yadda laifukan da suka shafi ƙasashe daban-daban da kuma safarar kuɗaɗen haram ke ƙaruwa, ya zama wajibi jami’ai su iya nazarin bayanan hada-hadar kuɗi, da bin diddigin kuɗaɗe ta dandamali daban-daban da kuma haɗa shaidun dijital da mutanen da ake bincike a kansu.
A nasa jawabin, jakadan hulɗa da ’yan sanda na Koriya ta Kudu a Najeriya, Eun-pyo Hong, ya ce wannan horaswa ita ce ta farko da gwamnatin Koriya ta Kudu ta gudanar a Afirka.
Ya ce shirin ya zo daidai da cikar shekara guda da sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin EFCC da Hukumar ’Yan Sandan Ƙasa ta Koriya ta Kudu (KNPA) a Seoul a watan Oktoba na 2025.
Shugaban tawagar masu horaswa daga Kwalejin Binciken ’Yan Sandan Koriya, Woosung Kwon, ya ce masu laifukan kuɗi na ƙara amfani da kuɗaɗen intanet, da fasahohin tura kadarori tsakanin blockchain daban-daban da kuma yanar gizo mai ɓoyayyen ɓangare wajen ɓoye kuɗaɗe.
Ya bayyana cewa horaswar za ta ƙunshi atisaye kan dabarun binciken bayanan da ake samu a fili, da bin diddigin kuɗaɗen intanet tun daga gano alamar farko har zuwa ƙwace kadarori da shirya shaidu domin gabatarwa a kotu.
Shugaban sashen hulɗa da ƙasashen waje na EFCC, Aliyu Wali, wanda ACE II Michael Kayang ya wakilta, ya ce ƙara wa jami’ai ƙwarewa wajen bin diddigin hada-hadar kadarorin dijital na da muhimmanci wajen yaƙi da laifukan kuɗi da ake aikatawa ta intanet da kuma dawo da dukiyoyin da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Ya buƙaci mahalarta horaswar su yi amfani da damar wajen musayar ilimi da takwarorinsu na Koriya ta Kudu, tare da amfani da abin da suka koya wajen gudanar da ayyukansu.