Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci sake zaɓensa a wa’adi na biyu saboda ya ɗauki matakai masu wahala a fannin tattalin arziki waɗanda gwamnatocin baya suka guje wa ɗauka.
Wike ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja ranar Talata, 13 ga Oktoba, 2026, inda ya ce Tinubu ya nuna jagoranci da ƙarfin hali wajen tunkarar manyan ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Ya kawo misali da cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya taimaka wajen samar da kuɗaɗen da jihohi ke amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa da biyan albashi.
Ya kuma ce ana biyan ’yan fansho, yayin da ɗalibai suka shafe shekaru uku ba tare da yajin aikin da ya hana su zuwa karatu ba.
- EFCC da ’yan sandan Koriya ta Kudu sun fara horas da jami’ai kan binciken kuɗaɗen haram da na intanet
- Majalisar Tarayya ta nuna goyon baya ga rundunar sojin sama bayan hatsarin jirgi
Dangane da korafe-korafen jama’a kan tsadar rayuwa, ministan ya ce sauya fasalin tattalin arzikin ƙasa ba abu ne da za a iya cimmawa cikin sauƙi ko nan take ba.
Ya bayyana cewa ana buƙatar ɗaukar matakai masu wahala, duk da cewa jama’a na iya fuskantar ƙalubale kafin su fara amfana da sakamakonsu.
Wike ya kuma kare kasancewar wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027.

Ya ce hakan ya nuna cewa goyon bayan shugaban ƙasa ya wuce jam’iyyar APC, yana mai cewa muradun ƙasa ya kamata su fi bambancin jam’iyya muhimmanci.
Ya ambaci gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, da gwamnan Osun, Ademola Adeleke, tare da kansa, a matsayin waɗanda ke da rawar da za su taka wajen tattara goyon baya ga Tinubu.
Ministan ya yi watsi da ra’ayin cewa masu goyon bayan shugaban ƙasa daga jam’iyyun adawa sai sun sauya sheƙa zuwa APC kafin su taimaka masa, inda ce ya bayyana wa magoya bayansa su goyi bayan Tinubu, kuma bai ga dalilin da zai haifar da rikici a cikin siyasar ƙasar ba.
Da yake magana kan ayyukan gwamnatinsa a FCT, Wike ya ce ya ziyarci dukkan ƙananan hukumomin gudanarwa guda shida na yankin, tare da bayyana cewa kowannensu yana da ofisoshin ’yan sanda biyu da gidajen zama na DPO.

Ya kuma ce ana sa ran ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa kafin Disamba, ciki har da hanyar Apo zuwa Karshi. Ministan ya ce masu ruwa da tsaki a FCT sun amince da goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027.
Wike ya kuma tabbatar da cewa an sanya hannu kan takardun shaidar sarauta da kayan aikin ofis na sarakunan gargajiya da aka ɗaukaka matsayinsu, inda ya ce za a gabatar musu da su nan ba da jimawa ba. Kan yajin aikin malaman makarantu a FCT kuwa, ya zargi shugabannin Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da amfani da yajin aikin domin cimma muradun siyasa, yana mai cewa za a warware matsalar bisa doka.
Haka kuma, ministan ya nemi tsohon gwamnan Ribas kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, da ya yi bayani kan ayyukan da ba a kammala ba da kuma kuɗaɗen da aka kashe a wasu ayyuka a jihar.
Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar zai iya samun goyon bayan dukkan Arewa a zaɓen 2027, yana mai cewa masu zaɓe za su yi la’akari da ayyukan ’yan takara da irin shugabancin da suka nuna, ba wai yankin da suka fito ba.
Game da siyasar Ribas da rawar Gwamna Siminalayi Fubara a haɗin gwiwar siyasa mai ɗauke da jam’iyyu daban-daban, Wike ya ce Fubara na cikin haɗin gwiwar kuma yana taka rawarsa.
Ya ƙara da cewa sun sasanta tsakaninsu tare da haɗa kai, yana mai cewa babban burinsu shi ne dangin siyasarsu su ci gaba da riƙe madafun iko a jihar.