Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce fasahar AI ba za ta maye gurbin ikon ’yan Najeriya wajen zaɓen shugabanninsu a 2027 ba.
Ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa kan fasaha da dimokuraɗiyya na shekarar 2026, inda ya ce za a iya amfani da fasahar wajen inganta jigilar kayan zaɓe, tsaro da sadarwa, amma ba za a bar ta ta yanke muhimman shawarwarin zaɓe ko tattara sakamako ba tare da sa hannun mutane ba.
- Gwamnatin tarayya ta goyi bayan shirin bunƙasa noma a ƙauyuka
- Mauritius ta sanya dokar hana fita bayan barkewar zanga-zanga
Amupitan ya yi gargaɗin cewa bidiyoyin ƙarya, da yaɗa labaran bogi da hare-haren intanet na iya barazana ga sahihancin zaɓe.
Ya ce INEC ta kafa sashe na musamman domin bibiyar irin waɗannan barazanar.
Ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa, da kafafen yaɗa labarai, da ƙungiyoyin fararen hula da jami’an tsaro da su haɗa kai wajen kare sahihancin zaɓen 2027, yana mai cewa hukumar za ta tabbatar da cewa ra’ayin ’yan Najeriya ne zai bayyana a sakamakon zaɓe.