Rundunar yan sandan Neja ta ce jami’an sashen yaƙi da manyan laifuka sun kama wasu mutum biyar a wurare daban-daban bisa zargin haɗin baki da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Waɗanda aka kama sun haɗa da wani matashi mai shekaru 23 daga jihar Kwara da mai shekaru 25 daga ƙauyen Zugurma a jihar Neja; da Legi Zangara,wani waɗanda shekarunsu suka kama daga 20 zuwa 20, daga jihar Kebbi.

Sanarwar ta ce mai shekaru 23 ya amsa cewa yana cikin ƙungiyar wani Gide da ake zargi da addabar al’ummomi a yankin ƙauyen Ibbi da babbar hanya, tare da amfani da dajin Ibbi a matsayin maboya.

Haka kuma, rundunar ta ce Hiri na aiki tare da wata ƙungiya da ake zargin wani Batijo ne ke jagoranta a dajin Gugu, yayin da Legi Zangara ya amsa cewa yana cikin ƙungiyar mutum bakwai da aka ɗauka domin yin garkuwa da wani mutum a watan Agusta, inda aka karɓi kuɗin fansa na naira miliyan 3.5.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Neja, CP Adamu Abdullahi Elleman, ya ce rundunar za ta ci gaba da yaƙi da manyan laifuka tare da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Ya kuma buƙaci jama’a su riƙa ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen hana aikata laifuka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *