Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta taya Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) da al’ummar Kiristoci murnar cika shekara 50 da kafuwa.
A cikin sanarwar da Babban Sakatarenta, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar a ranar 14 ga Oktoba, 2026, majalisar ta bayyana bikin a matsayin muhimmin ci gaba ba ga Kiristoci kaɗai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.
NSCIA ta ce shugabannin addinai da cibiyoyinsu sun taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya, tattaunawa da fahimtar juna tsakanin al’ummomin addinai daban-daban, duk da ƙalubalen da ƙasar ta fuskanta.
- ’Yan sanda sun kama mutum biyar kan zargin garkuwa da mutane a Neja
- An kama wani mutum bayan sare wa wani wuyan hannu a rikicin siyasa a Bauchi
- Masana sun bukaci a yi amfani da fasaha AI cikin gaskiya wajen zaɓen 2027
Majalisar ta jaddada cewa Musulmi da Kiristoci na da alhakin haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, adalci, tsaro da ci gaban ƙasa.
Ta kuma bayyana cewa matsalolin rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi da rashin daidaito na buƙatar haɗin kan dukkan ’yan Najeriya.
Ta ƙara da cewa bambancin addini bai kamata ya zama sanadin rarrabuwar kai, ƙiyayya ko tashin hankali ba, maimakon haka, koyarwar addinai ya kamata ta ƙarfafa adalci, tausayi da zaman lafiya.
NSCIA ta taya shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, da kwamitin zartarwa na ƙungiyar, da ƙungiyoyin addinin Kirista da Kiristoci a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja murna, tare da yi musu fatan samun hikima wajen gudanar da ayyukansu na ƙasa.